Lahadi 21 Afirilu 2024 - 22:20
Malaman Falsafa da Ilimin Hankali Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Farmakin “Wa’adus Sadiƙ” tare da Godiya ga Dakarun Sojin Musulunci

Hauza/ Malaman fannonin ilimin hankali da kuma mambobin Majalisar Ƙoli ta Ilimin Hikimar Musulunci sun yaba da kokarin dakarun sojin Musulunci, tare da bayyana goyon bayansu ga farmakin “Wa’adus Sadiƙ”. Sun kuma bayyana cewa suna ganin ya zama wajibi su yi cikakken bayani ta fuskar ilimi da siyasa kan wannan farmaki da manyan sakamakonsa, bisa tsarin tunanin siyasar Musulunci.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, wasu gungun malaman ilimin hankali da mambobin Majalisar Ƙoli ta Ilimin Hikimar Musulunci sun fitar da sanarwar goyon baya ga farmakin “Wa’adus Sadiƙ”. Ga fassarar cikakken abin da sanarwar ta ƙunsa:

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

“Lallai Mu, za Mu ɗauki fansa daga masu laifi.” (Suratus Sajdah: 22).

Muna miƙa gaisuwa da fatan samun rahamar Allah ga shahidai masu daraja, waɗanda suka ƙarawa ƙasarmu ta Musulunci ɗaukaka, girma da ƙarfi ta hanyar sadaukar da rayukansu da jininsu.

Haka kuma, muna miƙa gaisuwa da yabo ga dakarun sojin Musulunci da jaruman da suke ci gaba da kare martabar ƙasar nan cikin lura, basira da kyakkyawan shiri. Sun kasance a shirye wajen kare ƙasar, tare da mayar da martani mai ƙarfi ga duk wani mai neman kawo mata hari, kuma za su ci gaba da yin hakan.

Muna miƙa gaisuwa ta musamman ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kuma Babban Kwamandan Rundunonin Sojin Ƙasar, wanda jagorancinsa mai cike da hikima, hangen nesa da zurfin tunani ya kasance sanadin ƙara ɗaukaka, ƙarfi da martabar Iran ta Musulunci, da kuma ƙarfafa gwagwarmayar neman 'yanci da gwagwarmayar masu tsayin daka.

Bayan kisan wasu manyan kwamandojin dakarun Musulunci da na ƙungiyoyin gwagwarmaya, musamman harin wuce gona da iri da gwamnatin Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke ƙasar Siriya, wanda ya yi sanadin shahadar wasu manyan kwamandoji da masu ba da shawara na sojin Iran, jaruman rundunar kare juyin juya halin Musulunci, tare da haɗin gwiwar jaruman rundunar sojin ƙasa, Ma’aikatar Tsaro da sauran sassan soji, leƙen asiri, tsaro da yaɗa labarai, ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamandan Rundunonin Soji, sun tsara wani gagarumin farmaki mai muhimmanci da tsari mai zurfi, wanda aka yi wa suna “Wa’adus Sadiƙ”.

A yayin wannan farmaki, an kai hare-hare kan muhimman wurare a yankunan Falasɗinu da Isra’ila ta mamaye. Girman farmakin, faɗinsa da kuma ingancin tsarin shirinsa mai matakai daban-daban sun ba duniya mamaki.

Duk da cewa Amurka, ƙasashen Yamma da wasu gwamnatocin yankin da ba su da ƙarfin tsayawa da kansu, sun tattara dukkan ƙarfin kariya da taimakon soji da suke da shi, hakan bai rage girma ko tasirin wannan farmaki ba.

Nau’i, ƙarfi da tsananin hare-haren sun ƙara fito da ainihin ƙarfin da Isra’ila take da shi, tare da bayyana raunin ikonta na tsaro. Haka kuma, sun kawo ƙarshen yaɗa tunanin cewa “Garkuwar Ƙarfe” (Iron Dome) da tsarin kariyar tsaron Isra’ila ba sa iya karyewa.

Girma da nasarorin farmakin “Wa’adus Sadiƙ” sun haifar da sabon yanayi na alfahari, ƙarfafa kishin ƙasa da haɗin kan al'ummar Iran. Haka kuma, ya ƙara wa masu fafutukar neman 'yanci da Musulman duniya martaba da ƙima, tare da ƙarfafa gwiwar ƙungiyoyin gwagwarmaya da masu adawa da Isra’ila.

Babu shakka, wannan nasara babba ta shafi daukacin al'ummar Musulmi a duniya.

Muna miƙa godiya da yabo na musamman ga Allah Maɗaukaki, wanda Ya ba wa al'ummar Iran damar samun nasara da aiwatar da wannan gagarumin farmaki. Kamar yadda muka yi imani da cewa:

“Nasara daga Allah, kuma buɗi yana nan kusa.” (Suratus Saff: 13).

Haka kuma, muna sumbatar hannayen jaruman dakarun rundunar kare juyin juya halin Musulunci da rundunar sojin ƙasa, tare da yi wa matasan masana da masu bincike na rundunonin soji fatan ƙarin lafiya, ɗaukaka da nasara.

Malaman ilimin hankali da mambobin Majalisar Ƙoli ta Ilimin Hikimar Musulunci, bisa bin tafarkin manyan malamai, masana da maraji’ai, musamman manyan malaman da ke kula da majalisar, Ayatullah Jawadi Amuli da Ayatullah Subhani (Allah Ya ƙara musu lafiya da tsawon rai), suna bayyana godiyarsu ga dakarun sojin Musulunci tare da nuna goyon bayansu ga wannan gagarumin farmaki.

Haka kuma, sun bayyana cewa suna ganin wajibi ne su yi cikakken bayani ta fuskar ilimi da siyasa kan farmakin “Wa’adus Sadiƙ” da manyan sakamakonsa, bisa tunanin siyasar Musulunci.

Sun kuma yi kira ga dukkan marubuta, 'yan jarida, masu yaɗa labarai da masu jawabi, da waɗanda ke da kafafen isar da saƙo, da su yi cikakken bayani kan wannan farmaki, wanda suka bayyana a matsayin wani abin al'ajabi da ba kasafai ake samun irinsa ba a ƙarnukan baya-bayan nan. Sun kuma buƙaci a samar da ingantattun ayyukan yaɗa labarai da fasaha domin nuna wa duniya wani ɓangare na ƙarfin Iran, jarumtakarta da ƙarfin rundunonin sojojinta.

Yayin da muke bayyana cikakken goyon bayanmu ga jaruman dakarun rundunar kare juyin juya halin Musulunci da rundunar sojin ƙasa, muna roƙonsu da su kasance cikin shiri wajen mayar da martani cikin ƙarfi da hikima ga duk wani mataki ko hari da maƙiya za su kai wa muradun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a duk inda suke a duniya.

A ƙarshe, muna sake miƙa gaisuwa da fatan samun lafiya ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kuma Babban Kwamandan Rundunonin Soji. Muna kuma bayyana shirye-shiryenmu na bayar da gudummawa wajen kare Iran, juyin juya halin Musulunci da kyawawan manufofin addinin Musulunci.

Sunayen malaman da suka sanya hannu kan sanarwar:

Ayatullah Dakta Ahmad Beheshti

Ayatullah Sayyid Muhammad Gharawi

Ayatullah Ghulamreza Fayyazi

Ayatullah Alireza A’arafi

Hujjatul Islam wal Muslimin Hamid Parsania

Hujjatul Islam wal Muslimin Mohsen Qomi

Hujjatul Islam wal Muslimin Mojtaba Misbah

Hujjatul Islam wal Muslimin Hassan Mu’allimi

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali Zamani Qomshe’i

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali Abbasi

Hujjatul Islam wal Muslimin Yara’ali Firuzja’i

Hujjatul Islam wal Muslimin Reza Azariyan

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali Aghajani

Dakta Naƙi Akand

Hujjatul Islam wal Muslimin Alireza Al-Buyeh

Hujjatul Islam wal Muslimin Reza Ilahimanesh

Hujjatul Islam wal Muslimin Majid Abulƙasimzadeh

Hujjatul Islam wal Muslimin Hussain Ahmadi

Hujjatul Islam wal Muslimin Hussain Arjini

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali A’ala’i Banab

Hujjatul Islam wal Muslimin Mujtaba Afsharpour

Hujjatul Islam wal Muslimin Ahmad Zaki Afshagar

 Dakta Sayyid Abdulra’uf Afzali

Hujjatul Islam wal Muslimin Mahdi Omidi

Hujjatul Islam wal Muslimin Zuhair Ansariyan

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hussain Irandoust

Dakta Reza Bakhshayesh

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Safar Jibra’ili

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Ja’afari

Dakta Ghulamhussain Jawadpour

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hadi Jawadi Gilani

Hujjatul Islam wal Muslimin Reza Habibi

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hussainzadeh Yazdi

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Abulfazl Hussaini

Dakta Abulfazl Khurasani

Muhammad Baƙir Khurasani 

Hujjatul Islam wal Muslimin Mahdi Khayyatzadeh

Hujjatul Islam wal Muslimin Mustafa Daneshpajuh

Dakta Rahim Dehƙan

Dakta Sayyid Muhammad Ali Dibaji

Hujjatul Islam wal Muslimin Askar Deyrbaz

Hujjatul Islam wal Muslimin Sa’id Risalati

Hujjatul Islam wal Muslimin Izziddin Reza Nejad

Dakta Abulfazl Ruhi

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Jawad Rudgar

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Mahdi Zamani

Hujjatul Islam wal Muslimin Mahdi Zandiyeh

Hujjatul Islam wal Muslimin Abdulmajid Zahadat

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali Asghar Sam Daliri

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Amir Sakhavatyan

Hujjatul Islam wal Muslimin Jamal Soroush

Hujjatul Islam wal Muslimin Askari Sulaimani Amiri

Hujjatul Islam wal Muslimin Ruhullah Souri

Hujjatul Islam wal Muslimin Qasim Shabani Nia

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hussain Talebi

Dakta Is'haƙ Ɗahiri

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Muhammad Tabataba’i

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Alireza Tabataba’i

Abbas Arifi

Hujjatul Islam wal Muslimin Mahdi Abdullahi 

Dakta Hassan Abdi

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Arab Salihi 

Dakta Ramazan Ali Tabar Firuzja’i

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Sadik Alipour

Hujjatul Islam wal Muslimin Abulhassan Ghaffari

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hadi Fazel

Hujjatul Islam wal Muslimin Ahmad Farbahi

Hujjatul Islam wal Muslimin Asadullah Firuzja’i

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Reza Qadiri

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hassan Qadrdan

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Baƙir Qayyumi

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali Karshenas

Hujjatul Islam wal Muslimin Mahdi Karimi

Dakta Abulfazl Gha’ini

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Mahdi Gorjian

Hujjatul Islam wal Muslimin Jawad Goli

Dakta Sharif Lakza’i

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Taƙi Rukni Lamuqi

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Reza Mostafapour

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Jabir Mousavi Rad

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Mahmoud Mousavi

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhsin Mohajernia

Dakta Alireza Mirza'i

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Muhammad Mirhashemi

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Hussein Na'iji

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Abazer Nabavian

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Ali Nouri

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Jawad Norouzi

Hujjatul Islam wal Muslimin Ali Nahavandi

Dakta Muhammad Ali Niazi

Hujjatul Islam wal Muslimin Vahid Vahed Chovan

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Morteza Honarmand

Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Taqi Yusifi

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha